Wani tsohon jami’in tsaron haramtacciyar Kasar Isra’ila ya bayyana cewa, an kawo karshen yaki da Isra’ila ta fadi kasa warwas, yayin da kungiyar Hamas ta sami nasara.
Bayan gushewar kwanaki 470 na yakin kare dangi da HKI ta shelanta akan mutanen Gaza, tsohon shugaban Majalisar tsaron HKI, Giora Iland ya ce, tabbas Hamas ta sami nasara a wannan yakin.
Iland ya furta haka ne a wata hira da ya yi da tashar talabijin din ta 7; da marecen jiya Asabar, ya ce, zan yi kari akan abinda na fada a baya, na cewa ba a cimma manufar yakin ba, domin duk tsananin hare-haren da aka kai wa Hamas, bai kawo karshenta ba, kuma ba a kwato fursunoni ba.
A jiya Asabar din dai ‘yan share wuri zauna sun yi zanga-zanga a birnin Tel Aviv na nuna kin amincewarsu da tsagaita wutar yaki a Gaza da kuma nuna kin amincewa da musayar fursunoni.
Masu Zanga-zangar sun bukaci ganin ba a yi aiki da tsagaita wutar yaki ba,da kuma musayar fursunoni da suke ganin cewa za ta sa nasarar da ‘yan sahayoniyar su ka samu ta salwanta.
A can birnin Kudus ma dai ‘yan share wuri zauna din sun yi kira ga sojojin HKI da su ci gaba da yin kisan kiyashi a Gaza kafin ace an isa ga aiki da tsagaita wutar yaki.