Shugaban Amurka Donald Trump, ya katse tallafin da yake baiwa jami’ar Columbia saboda zanga-zangar goyan bayan Falasdinu.
Trump ya ce an katse tallafin na dala miliyan 400 ga jami’ar, daya daga cikin manyan a kasar, bisa zarginta da gazawa wajen fuskantar ayyukan kyamar Yahudawa a harabarta, wanda ke nufin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.
Ana kallon wannan a matsayin alwashin da Donald Trump, ya sha a lokacin yakin neman zabe inda sha yin tir da yadda wasu jami’o’i ke nuna gazawa wajen fuskantar zanga zangar goyan bayan Falasdinu.
Masana da dama na ganin matakin a matsayin misali na siyasantar da manyan makarantu da kuma tsoma bakin gwamnati.
Shugaban kungiyar jami’o’in Amurka ya bayyana cewa matakin na gwamnatin Trump “ya haifar da matukar damuwa game da sha’anin ilimi da kundin tsarin mulkin Amurka kan ‘yancin fadin albarkacin baki.
Dama Trump ya sake nanata barazanarsa a wannan makon, inda ya yi alkawarin rage kudaden da ake ba duk jami’ar da ta ba da damar gudanar da zanga-zanga ba bisa ka’ida ba.