Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya na cewa rashin halartar kasashen Rasha da China a cikin duk wata tattaunawa dangane da shirin Nukliyar kasar Iran, zai kawo gibi mai yawa a harkokin siyasa da tsaro a yankin Asiya.
Jami’in diblomasiyyan ya kara da cewa kasahen yamma suna son maida kasashen biyu gefe a cikin tattaunawar, a yayinda kasancewarsu a cikin taron yana da matukar muhimmanci saboda al-amarin zai shafi yankin gaba daya.
Daga karshe jakadan ya kammala da cewa ya na fatan tattaunawa dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran, zai ci gaba ne a cikin kasashe 5+1 kuma rashin halattan kasashen Rasha da China zai hana duk abinda bangarorin biyu suka tattauna ko suka cima matsayin a kansa ya kasa tafiya kamar yadda ya dace.