Yiyuwar shugaban Joe Biden na kasar Amurka ya ci gaba da zama dan takarar shugaban kasa wa jam’iyyarsa ta Democrats ya na kara shiga cikin hatsari bayan da wani dan majalisar dokoki a Jam’iyyar ya bukaci ya kauce daga yin takarawa jam’iyyar ya bawa wanda ya dace.
George Clooney da wasu manya manyan yan jam’iyyar ta Democrats sun bayyana cewa Biden, bai da lafiyan da zai tsayawa jam’iyyar takarar shugaban kasa.
Clooney ya kara da cewa, ya zauna da shugaban kasan a cikin watan da ya gabata, ya kuma gano cewa Joe Biden a yanzun ba shi ne, joe biden a shekara ta 2020 ba.
Jaridar NewYork times ta bayyana cewa ana ci gaba da takurawa shugaban ya janye ya kuma bawa wanda yake da koshin lafiya a jagorancin jam’iyyar a zaben watan Nuwamba mai zuwa, idan ba haka ba zai jawowa jam’iyyar wata musiba ce.
A muhawar da shugaban yayi da abokin hamayyarsa na jam’iyyar Republican wato Donal Trump ya nuna cewa shugaban yana da matsala a maganganunsa da kuma karfin kwakwalwansa. Don haka tsofa da kuma rashin lafiyeyyen kwakwalwa suna damunsa.