Amurka Ta Yi Barazana Ga Ukraine A Dai-dai Lokacinda Ta Fitar Da Shirin Zaman Lafiya Da Rasha Na Karshe

Gwamnatin kasar Amurka ta gargadi kasar Ukraine a dai dai lokacinda ta gabatar da shirin zaman lafiya da kasar Rasha na karshe. Shirin da shugaban

Gwamnatin kasar Amurka ta gargadi kasar Ukraine a dai dai lokacinda ta gabatar da shirin zaman lafiya da kasar Rasha na karshe.

Shirin da shugaban kasar Donal Trump ya bayyana shi ne karshe dai, ya bukaci gwamnatin shugaba Volodimir Zelesky ta amince da yankin Cremea da kuma sauran yankunan hudu wadanda Rasha ta mamaye da karfi shekaru uku da suka gabata su zama mallakin kasar Rasha har’ abada. Sannan ta amince a daukewa kasar Rasha takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata tun bayan fara yakin. Sannan daga karshe ta amince ba zata shiga kungiyar tsaro ta NATO ba.

Shawara bata yi maganar wani abu banada wadannan hudu ba, duk da cewa Ukraine tana da wasu bukatu a yarjeniyar tsagaita wuta da kuma samar da sulhu mai dorewa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Moscow ta bukaci a tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu don samun damar tattaunawa amma gwamnatin Kiev ta ki amincewa.

Masana suna ganin wadannan al-amura suna da nauyi ga kasar ta Ukraine, amma kuma bata da zabi tunda Amurka ce ta biya mafi yawan kudaden da Ukraine ta kashe a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments