Kwamitin tsaro na MDD a jiya Alhamis 18 ga watan Satumba, ta kasa samun wani kuduri wanda kenufin tabbatar da zaman lafiyaa gaza da kuma tsagaita wuta a dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka wacce take da hakkin hawan kujeran na ki wato Veto ta haka kudurin wucewa.
Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto dan rahotonta a NewYork yana cewa dalilan da gwamnatin Amurka ta bayar na hana wannan kudurin wucewa sun hada da abinda ta kira rashin yin allawadai da kungiyar Hamas da kuma da kuma ambatun hakkin HKI na kare kanta a gaban hamas.
Kafin haka dai ta sami amincewar dukkan sauran mambobin kwamiton tsaron 14. Jami’an diblomasiyya sun bayyana cewa, ba wannan ne karon farko wanda Amurka take amfani da hakkin Veto don haka zaman lafiya a kasar Falasdinu da aka mamaye ba. Kuma mai yuwa ba zai zama na karshe ba.
A cikin shekaru 2 da suka gabata, Amurkata hana zaman lafiya a Gaza har sau 6 saboda kare yahudawan sahyoniyya.