Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin  Gaza da Afghanistan

Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta yi gyara ga yarjejeniyar da aka kafa domin

Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta yi gyara ga yarjejeniyar da aka kafa domin kare Trump da manyan jami’an Amurka daga duk wani bincike na yanzu ko nan gaba, in ji wani jami’in gwamnatin Trump a ranar Laraba. Barazanar dai na kunshe ne da gargadin kara sanya takunkumi idan kotun ta ki bin umarnin.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, wa’adin na Washington ya hada da karin wasu bukatu guda biyu: cewa kotun ta ICC ta janye bincikenta kan laifukan yaki da shugabannin Isra’ila suka aikata a lokacin yakin Gaza, da kuma cewa ta rufe binciken da ta yi tun farko kan halin sojan Amurka a Afghanistan. Idan kotu ta ki yin aiki, gwamnatin Amurka  na iya sanya sabbin takunkumi kan daidaikun jami’an ICC.

Matsayin gwamnatin Trump na baya-bayan nan ya ginu ne kan takun saka a baya da hukumomin kasa da kasa. Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague, ta fuskanci matsin lamba daga Washington tun bayan da ta bude bincike kan ayyukan sojan Amurka a lokacin yakin Afghanistan da kuma a baya-bayan nan, kan matakin da “Isra’ila” ta dauka a zirin Gaza.

Jami’an Trump sun bayyana irin wannan binciken a matsayin na siyasa da kuma cin zarafi ga ikon kasa, kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted