Gwamnatin amurka ta kwace kudaden Jami’ar Calfoniya da ke birnin Losangelis saboda abinda ta kira samuwar masu goyon bayan Falasdinawa a cikin dalibai da kuma malaman jami’ar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wannan babban kalu bale ne ga Jami’ar saboda rashin wadan nan kudade. Amma gwamnatin amurka ta na zargi hukumomin Jami’ar da gudanar da barin a gudanar da tarurruka da kuma gangami da zanga zanga na goyon bayan Gaza a jami’ar.
Labarin ya nakalto Dr Julio Frenk shugaban Jami’ar Calfonia a birnin Losangeles na 7th ya bayyana a jiya Laraba kan cewa rike wadannan kudin ba karami matsalace ga Jami’ar UCLA ba, ga kuma kasar Amurka kanta.
Gwamnatin nTrump dai ta bayyana cewa Jami’ar LosAngeles a Califonia, da, Columbia University a New Yrork da Stanford University, da wasu da dama a Amurka suna barin a gudanar da ayyukan na kin yahudawa a cikinsu. Wadanda suka hada da taron gangamin yin All..wadai da HKI da kuma gwamnatin Amurka wacce take goyon bayanta a kissan kiyashin da take yi a Gaza.
Wannan matsalar ta bullowa wadannan jami’o’I ne tun lokacin fara yakin Tufanul Aksa a shekara ta 2023.