Amurka Ta Dakatar Da Karatun Wasu Daliban Jami’ar Michigan Saboda Goyon Bayan Falasdinawa A Gaza

Jami’ar Michigan ta Amurka ta dakatar da karatun wasu daliban jami’ar saboda rawar da suka taka, a zanga-zangar goyon bayan Gaza a yakin watanni 15

Jami’ar Michigan ta Amurka ta dakatar da karatun wasu daliban jami’ar saboda rawar da suka taka, a zanga-zangar goyon bayan Gaza a yakin watanni 15 da suka yi da HKI.

Kamfanin dillancin labaranSahab ya nakalto kamfanin dillancin labaran Mehr yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, hukumar Jami’ar Michigan ta kori wasu daliban daga karatu har na tsawon shekaru biyu.

Labarin ya nakalto hukumomin Jami’ar na cewa, wadannan daliban sune suka shirya zanga-zanga a cikin Jami’ar, inda suka maida ita cibiyar goyon bayana Falasdinawa a Gaza.

Ta kuma kara da cewa wannan kin kabilar samiyawa ne.

Jami’ar ta sa an kama wasu malaman jami’ar, ta kuma dakatar da wasu daga karantarwa, sannan wasu kuma an koresu daga jami’an kwatakwata.

Kafin haka dai shugaba Trump ya sha alwashi ladabtar da dalibai da kuma malaman Jami’o’ii a kasar wadanda suke nuna adawa da HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments