Amurka Ta Aika Makamai Zuwa Tarayyar Najeriya Don Yaki Da Yan Ta’adda

Gwamnatin Amurka ta aike da makamai zuwa tarayyar Najeriya a cikin shirin ta na taimakawa kasar yaki da kungiyoyin yan ta’adda a kasar wacce ta

Gwamnatin Amurka ta aike da makamai zuwa tarayyar Najeriya a cikin shirin ta na taimakawa kasar yaki da kungiyoyin yan ta’adda a kasar wacce ta ce suna kashe kiristoci tsiraru a kasar.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto majiyar ‘United State Africa Command ko (AFRICOM) na tabbatar da wannan labarin a yau Talata a shafinta na X. AFRICOM dai tana bada wannan sanarwan ne, a matsayinta na hukuma wacce take kula da al-amuran tsaro na Amurka a nahiyar Afrika.

Tun lokacinda shugaban Amurka Donal Trump ya yi barazanar kaiwa mabuyan yan ta’adda a Najeriya hare-hare, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci hadin kai da ita don yakar yan ta’addan da suka addabi kasar tun shekara 2009.

Wasu masana sun bayyana cewa ya zuwa yanzu yan ta’adda daga kungiyoyi daban-daban a tarayyar Najeriya sun kashe mutane kimani 40,000 a duk  fadin kasa, mafi yawansu musulmi daga kuma arewacin kasar.

A daren kirsimetin da ya gabata jiragen yakin Amurka sun kai hare hare kan wasu wurare a arewacin Najeriya wadanda suka hada da jihar sokoto da kuma Naija.

Kafin haka dai trump na zargin gwamnatin Najeriya da kashe kiristoci tsiraru a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted