Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi gargadin cewa amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi na samar da kudirorin doka da nufin tsawaita ikon Isra’ila a gabar yammacin kogin Jordan “barazana ne ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya shaidawa manema labarai a lokacin da yake shirin tafiya Isra’ila cewa, ” wannan ba wani abu ne da za mu iya ba da goyon baya gare shi ba a wannan lokaci.”
Furin nasa na zuwa ne bayan da majalisar dokokin Isra’ila ta kada kuri’a kan samar da wani kudirin mallake Gabar Yamma da Kogin Jordan a matsayin yankin Isra’ila.
Kudirin wanda wani dan majalisar Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi ya gabatar na zuwa ne a daidai lokacin da mataimakin shugaban Amurka JD Vance ke ziyara a kasar domin tattauna batun tsagaita wuta a Gaza.
A watan da ya gabata, Shugaba Trump ya ce ba zai bari Isra’ila ta mamaye yankin ba, wanda Falasdinawa ke kallo a matsayin tasu kasar.
Amurka dai na son a ci gaba da shirin kafa rundunar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa da kafa sabuwar gwamnati a Gaza da kuma kwance damarar Hamas, wanda ke cikin mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da Isra’ila.