Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto wata majiya biyu tana nuni da Shirin kamfanin na dakatar da ayyukansa, bayan gajiyawa wajen tseratar da shi.
Shi kuwa kamfanin dillancin labarun “Assiciated Press” kamfanin zai dakatar da ayyukansa ne bayan da ya durkushe, kuma hauhawar farashin makamashi saboda yaki akan Iran, ya taka rawa.
Da akwai ma’aikata 17,000 da suke aiki a karkashin kamfanin da rushewarsa zai sa su zama marasa aikin yi.