Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi Isra’ila da ta gaggauta dakatar da siyasar amfani da karfi na yi wa Falasdinawa karfa-karfa a yammacin kogin Jordan. Hakan nan kuma ta yi kira ga HKI da ta daina ayyukan da za su iya zama azabtar da al’umma kaco kau.
Kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta kuma bayyana cewa, irin wannan siyasar da Isra’ilan take amfani da ita, ta tilasata wa Falasdinawa 40,000 yin hijira daga yammacin kogin Jordan.
Hukumar ta “Amnesty” ta sanar a yau Alhamis cewa; Falasdinawa mazauna “Budhum” a Musafir suna fuskantar hatsarin korarsu a kurkusa saboda yadda ‘yan share wuri zauna suke kai musu hare-hare a karkashin kariyar hukumar ‘yan sahayoniya. Har ila yau ana rushewa Falasdinawan gidajensu da kuma takura musu matuka idan suna son shiga wurin wasu yankunan na Falasdinu.
Wata daga cikin matsalolin da Falasdinawan suke fuskanta kamar yadda “Amnesty” ta bayyana, ita ce yadda Isra’ila take gina sabbin matsugunan ‘yan share wuri zauna.
HKI tana son korar Falasdinawa daga yammacin kogin Jordan da kuma Gaza, kuma tana samun goyon bayan gwamnatin Amurka ta Donald Trump.