Al’ummomi Daga Sassan Duniya Suna Yin Tofin Allah Tsine Kan Sace Masu Fafatuka A Kan Hanyarsu Ta Zuwa Gaza 

Al’ummu daga dukkan sassan duniya suna mayar da martaninsu cikin fushi bayan sace jirgin ruwa Madeleine mai dauke kayayyakin jin kai zuwa Gaza Kwamandojin sojojin

Al’ummu daga dukkan sassan duniya suna mayar da martaninsu cikin fushi bayan sace jirgin ruwa Madeleine mai dauke kayayyakin jin kai zuwa Gaza

Kwamandojin sojojin mamayar Isra’ila sun yi garkuwa da jirgin ruwan farare hula Madeleine, wanda ke yunkurin karya killace yankin Zirin Gaza da aka yi a kokarinsu na shigar da kayan agaji ga al’ummar yankin da suka rage. Sojojin mamaya sun garkuwa da masu fafutuka tare da kai su tashar ruwan Ashdod. Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin yankin sun yi tir da laifin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata. Kungiyar Hamas ta bayyana shi a matsayin ta’addancin kasa da kasa.

A wani sabon laifin da ya saba wa dukkanin ka’idojin kasa da kasa da na jin kai, sojojin mamayar Isra’ila sun yi awon gaba da jirgin ruwan da kekokarin karya killace Gaza na Madeleine, tare da yin awungaba da masu fafutuka na kasa da kasa da ke cikin jirgin. Jirgin yana kan hanyar zuwa zirin Gaza dauke da kayan agaji ne.

Sojojin mamaya sun kai jirgin zuwa tashar jiragen ruwa ta Ashdod domin yi wa masu fafutuka tambayoyi tare da tabbatar da ko su wane ne su, har zuwa lokacin da ake yi musu tambayoyi a wani sansanin sojin ruwa da ke tashar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted