Al’ummomi A Duniya Na Farin Ciki Da Hare-Haren Martanin Iran Kan Isra’ila

Bayan kaddamar da harin martani da makamai masu linzami da kasar Iran ta yi a kan haramtacciyar kasar Isra’ila a yammacin jiya Talata, dubun dubatar

Bayan kaddamar da harin martani da makamai masu linzami da kasar Iran ta yi a kan haramtacciyar kasar Isra’ila a yammacin jiya Talata, dubun dubatar mutane sun fito a kasashe da dama domin nuna murna da farin cikinsu kan matakin na Iran.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, matakin da Iran ta dauka na mayar da martani da makami mai linzami kan zaluncin gwamnatin sahyoniyawan da ta shafe shekara guda tana yi a yankin da kuma kan fararen hula a Lebanon da Gaza, da kuma kisan gillar da aka yi wa Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah, da Isma’il Haniyyah, shugaban ofishin siyasa na Hamas, hakan ya faranta rayukan al’ummar Falasdinawa.

A faifan bidiyon da aka watsa a kafafen yada labarai, bayan yada labarin mayar da martani da makami mai linzami da Iran ta yi kan laifukan da gwamnatin sahyoniyawan ta aikata a baya-bayan nan, al’ummar Gaza sun yi ta nuna farin ciki a kan titunan yanki domin nuna goyon baya ga mataki na Iran.

‘Yan gudun hijirar Palastinawa sun taru kan tituna suna murna saboda harin da Iran ta kai kan yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye da matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna .

Har ila yau al’ummar kasar Yemen sun fito kan tituna bayan harin makami mai linzami da Iran ta kai kan gwamnatin sahyoniyawa.

A cewar hotunan da tsahr al-Masira ta bayar, al’ummar kasar Yemen na rera taken kyamar zaluncin gwamnatin yahudawan sahyoniyawa a kan al’ummar Falastinu da ma sauran al’ummomin yankin baki daya.

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci a cikin wata sanarwa da suka fitar sun  ce: “A matsayin martani da daukar fansar jinin shahidai Isma’il Haniyyah, Sayyid Hasan Nasrallah da Janar Nilfroshan, sun kai hari a tsakiyar yankunan Falastinawa da yahudawa suka mamaye, da kuma a kan sansanonin soji guda uku da cibiyoyin leken asiri na Mossad a birnin Tel Aviv.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments