Al’ummar Tunusiya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Falasdinawa

Al’ummar Tunisiya sun fito zanga-zangar yin Allah wadai da kisan kiyashin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a Gaza Al’ummar Tunusiya sun gudanar da

Al’ummar Tunisiya sun fito zanga-zangar yin Allah wadai da kisan kiyashin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a Gaza

Al’ummar Tunusiya sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da ci gaba da yakin kisan kiyashi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a Zirin Gaza, tare da jaddada nuna goyon bayansu ga gwagwarmayar Falasdinawa.

Al’ummar Tunusiya sun gudanar da zanga-zangar ce babban birnin kasar Tunis, suna rera taken mutuwa ga ‘yan sahayoniyya da masu goya musu baya musamman gwamnatocin Amurka da wasu kasashen yammacin Turai tare da addu’ar Allah ya bada da nasara ga al’ummar Falasdinu da suke dandana kudarsu.

Khudari ya kara da cewa: Mun zarce shahidai 43,000 da kuma wasu fiye da 100,000 da suka samu raunuka a Gaza, baya ga wadanda suka bace a karkashin baraguzan gine-gine, kuma ba mu san adadinsu a yankin ba, baya ga shahidai fiye da 3,000 a kasar Lebanon.

Babban jami’in gudanarwa na kungiyar taimakon Falasdinawa Bashir Khadhari ya bayyana cewa: A halin yanzu haka yawan Falasdinawa da suka yi shahada sun haura dubu 43, sanna wadanda suka jikkatasun fi dubu 100 a Gaza baya ga dubban wadanda suka bata, yayin adadin wadanda suka yi shahada a kasar Lebanon suka haura dubu 3.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments