Al’ummar Iran Ba Zasu Amince Da Ci Gaba Da Zaman Tattaunawa Da Amurka Ba Saboda Fushin Da Suke Ciki Na Kai Musu Hari

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Babu wanda ko da a kuskure ya yi magana a kan tattaunawa da Amurka saboda tsananin fushin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Babu wanda ko da a kuskure ya yi magana a kan tattaunawa da Amurka saboda tsananin fushin da al’ummar Iran ta yi

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya ce dangane da tattaunawar da aka yi da Amurka, “A halin yanzu al’ummar Iran suna cikin fushi matuka, ta yadda babu wanda ya isa ya yi magana kan batun gudanar da zaman tattaunawa da Amurka ko harkar diflomasiyya.”

A cikin wata hira da gidan talabijin na Sky News, yayin da yake mayar da martani kan wata tambaya kan shirin nukiliyar Iran biyo bayan harin wuce gona da iri da Amurkawa da ‘yan sahayoniyya suka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, Baqa’i ya ce: “Sun yi imani da farko dole ne su fahimci abin da ya faru, kwarai abin da ya faru shi ne wani danyen aikin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi aikata kan kasar Iran, sannan kuma Amurka, kan ‘yancin kan kasar Iran da kuma ikon kasar.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments