Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale
A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a gare shi) ya jagoranta, a cikin wadannan shekaru da dama, juyin juya halin Musulunci ya fuskanci makirce-makirce masu yawa da cikas, kuma ya samu gagarumar nasara, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne hambarar da gwamnatin sarki Shah da kasashen yammacin duniya suke goya masa baya, kamar yadda Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci ta yi nasarar kafa gwamnati da samar da ginshikanta da samun gagarumar nasarori da ci gaba a dukkanin fannonin kimiyya da fasaha, kuma Iran ta zama daya daga cikin kasashen da suka ci gaba a duniya.
A shekara ta 1979 ne duniya ta shaida wani lamari na juyin juya hali na duniya wanda ya sauya fasalin duniya tare da bai wa Imam Ayatullah Ruhollah Khomeini (amincin Allah ya tabbata a gare shi) nasarar kifar da gwamnatin kama karya mafi zalunci mai karfin alaka ta kud da kud da kasashen yammacin Turai ta Sarki Shah Mohammad Reza Pahlavi da ya dauki matakin gudu daga Iran zuwa abokansa musamman Amurka sannan ya yi gudun hijira zuwa kasar Masar bayan da ya fuskancin juya baya ga iyayen gijinsa na yammaci Turai.
Juyin juya halin Musulunci ya samar da sabon daidaito ta hanyar kafa ma’auni na kasa da kasa tare da kafa kasa mai cin gashin kanta da ta ‘yantar da kanta daga wadanda suke juya akalar duniya a wancan lokacin wato Amurka da Tarayyar Soviet.