Almayadin Ta Sami Rahoton Hukumar Makamashin Ta Duniya  ( IEA)  Aka Cewa Iran Tana Aiki Da Dukkanin Ka’idoji

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta fitar da wani rahoto da shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya fitar da a ciki

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta fitar da wani rahoto da shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya fitar da a ciki yake tabbatar da cewa, Iran tana aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta.

Rahoton dai ya kunshi cewa, tun bayan yarjejeniyar birnin Alkahira na kasar Masar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran da kuma shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa Refael Grossy, Iran din ta yi aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta.

Grossi ya rubutawa Iran wasika a ranar 7 ga watan Nuwamba na 2025 yana mai cewa; Bayar da dama ga hukumar domin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a cikin Iran, yana a matsayin aiki ne da nauyin da ya rataya a wuyanta kamar yadda yarjejeniyar da aka kulla ta tanada.

A ranar 11 ga watan Nuwamba na 2025 Iran aike wa  hukumar ta ambaci cewa: Bai wa hukumar ta makamashin Nukiliya ta kasa da kasa hadin kai, zai kasance bisa matakin da Majalisar koli ta tsaron kasar Iran za ta dauka. Haka nan kuma ta ambaci cewa Hkumar ta gudanar da bincke har sau 11 wanda ya fara a karshen watan Ogusta na 2025.

Bugu da kari Grossy ya sake aike wa Iran da wata wasikar a ranar 7 ga watan Nuwamba  da a ciki yake bukatar Iran ta yi bayani akan barnar da hare-haren Isra’ila da Amurka su ka yi wa cibiyoyin Nukiliyar.

Wani sashe na rahoton ya ce Iran tana baytar da hadin kai akan gudanar da bincike da kuma bayar da bayanai akan yadda tsarin ginin cibiyoyin yake.

A ranakun 19 zuwa 21 ne majalisar gwamnonin hukumar suke yin taron shekare-shere, kuma a can ne ake sa ran gabatar da wannan rahoton

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments