Al-Mayadeen: Ziyarar Larijani a Siriya da Lebanon na dauke da muhimman sakonni

Majiyar tashar Al-Mayadeen ta bayyana cewa, ziyarar da babban mai baiwa jagoran juyin juya halin Musulunci da Jumhuriya Ali Larijani  a kasashen Siriya da Labanon

Majiyar tashar Al-Mayadeen ta bayyana cewa, ziyarar da babban mai baiwa jagoran juyin juya halin Musulunci da Jumhuriya Ali Larijani  a kasashen Siriya da Labanon na zuwa ne bisa tsarin siyasa na musamman.

Majiyar ta bayyana cewa, babban mai bayar da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran yana dauke da muhimman sakonni ga kasashen biyu.

Larijani ya isa Damascus babban birnin kasar Syria a yau Alhamis, domin ganawa da shugaban kasar Bashar al-Assad da kuma manyan jami’an kasar ta Syria.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baghaei ya bayyana a yammacin jiya Laraba cewa: Larijani ya jagoranci wata tawaga a hukumance, kuma abin da ziyarar za ta fi mayar da hankali a yayin  ganawarsa da jami’an kasar Syria, ya shafi halin da ake ciki a yankin da kuma dangantaka tsakanin Iran da Syria.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments