Al-Husy: Yakin Gaza Shi Ne Kisan Kiyashi Mafi Muni A Cikin Karni Daya

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin  da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon  watanni 19 a

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin  da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon  watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni  akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya.

Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda yake faruwa a tsakiyar duniyar musulunci,kuma dukkanin duniya tana Kallon abinda yake faruwa. Shugaban na kungiyar Ansarullah ya kuma ce, a baya, ba a Kallon laifuka irin wadannan kai tsaye ta talbijin amma a yanzu ana Kallon ta akwatin talabijin.

Shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya kuma yi gargadin cewa da akwai sakamakon da zai biyo bayan wadannan manyan laifuka,yana mai kara da cewa. Alummar musulmi, a sahun gaba larabawa suna da alhakin abinda yake faruwa.

Haka nan kuma ya jaddada cewa  babu wani dalili da zai sa a yi watsi da jihadi saboda Allah da kuma kalubalantar azzalumai, sannan ya kara da cewa, yin watsi da wannan farilla mai tsarki, zai iya jefa al’umma cikin  fushin Allah madaukakin sarki, da hakan yake tattare da mummunan sakamako a duniya da lahira.

Sayyid Abdulmalik ya kuma bayyana cewa; Ci gaba da kau da kai da al’umma take yi akan abinda yake faruwa a Gaza, bai dauke mata nauyin da ya rataya a wuyanta ba,yana mai kara da cewa; Sakamakon da za a fuskanta daga Allah yana karuwa gwargwadon yadda ake samun koma-baya wajen yin abinda ya kamata akan al’ummar Falasdinu.

Akan tsayin dakar al’ummar Falasdinu kuwa, shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya jaddada cewa, ‘yan gwgawarmaya suna da dukkanin abinda suke bukatuwa da shi domin ci gaba da fuskantar ‘yan sahayoniya. Ya kuwa jinjinawa gwagwarmayar da kuma al’ummar Falasdinu baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments