Al-Houthi: Kisan jami’an fararen hula manuniya ce kan gazawar Isra’ila

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a birnin San’a wanda ya kai ga shahadar firaministan kasar Yemen da wasu jami’an farar hula da dama.

A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na jinjinawa shahidai, al-Houthi ya bayyana cewa, “laifi na kai hari kan ministoci da ma’aikatan farar hula ya kara tabbatar da laifukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankin,” yana mai jaddada cewa dukkan wadanda suka yi shahada suna gudanar da ayyukansu ne a fagagen da ba na soja ba.

Da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalan shahidai, abokan aikinsu, da al’ummar kasar Yemen, ya tabbatar da cewa wuce gona da iri ba zai karya azamar al’ummar kasar Yemen ba.

Al-Houthi ya tunatar da cewa, wannan sabon harin wani bangare ne na wuce gona da iri, yana mai cewa: “Wadannan  suna daga cikin irin  munanan laifuka da Isra’ila take aikatawa a kan al’ummar Palastinu, Lebanon, Siriya, Iraki da Iran.” Ya yi tir da irin wanann  zaluncin da kekasar zuciya,  yana mai cewa, Isra’ila ta wuce dukkanin iyakoki, kuma dole ne ta fuskanci sakamakon ayyukanta.”

Ya jaddada cewa irin wadannan laifuffukan suna nuna mahimmanci da wajabcin yin gwagwarmaya domin dakile manufofinta a cikin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments