Al-Houthi: Hare-haren Amurka sun kasa dakatar da gwagwarmayar Yeman

Madugun kungiyar Ansarallah ta kasar Yeman ya yi ikirarin cewa, zafafan hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kasar Yemen, ya kasa dakatar

Madugun kungiyar Ansarallah ta kasar Yeman ya yi ikirarin cewa, zafafan hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kasar Yemen, ya kasa dakatar da ayyukan gwagwarmayar Yeman na goyon bayan al’ummar Gaza ko kuma kare jiragen Isra’ila a tekun Bahar Rum.

A wani jawabi da ya yi a ranar Juma’a, Abdul-Malik al-Houthi ya ce Amurka ta zafafa kai hare-hare a kan kasar Yemen, inda wasu lokutan ta kai hare-hare sama da 90 a kowace rana, a wani bangare na goyon bayan da take baiwa kasar Isra’ila a yakin kisan kare dangin da ta ke yi a zirin Gaza.

Duk da haka, ya jaddada cewa, hare-haren na Amurka “sun kasa dakatar da ayyukan soji da ke tallafawa al’ummar Falasdinu, ko kuma tabbatar da kare zirga-zirgar jiragen ruwa na Isra’ila a cikin Bahar Maliya, Gulf na Aden da kuma Tekun Oman.”

Ya kuma ce jami’an sojin Amurka sun amince cewa hare-haren sun kasa dakile karfin sojojin Yemen.

Al-Houthi ya ce: “Amurka ta gaza cimma burin da ta sanya a gaba na kawar da shugabanni da kuma kawar da ‘yantacciyar kasar Yemen.”

Ya yi alkawarin cewa kasar Yemen za ta ci gaba da kai hare-hare na daukar fansa, kafin ya bayyana cewa: “Amurka ba ta tsoratar da mu.”

Shugaban kungiyar Ansarallah ya kuma gargadi gwamnatocin kasashen Larabawa da kasashen da ke makwabtaka da su kan goyon bayan hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen sannan ya kara da cewa kutsawar da Ministan Isra’ila mai tsatsauran ra’ayi, Itamar Ben-Gvir ya yi a harabar masallacin Kudus, shaida ce ta ci gaba da cin zarafi da Isra’ila ke yi kan “daya daga cikin mafi girman wurare masu tsarki ga musulmi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments