Al-Burhan: Sojojin Sudan Sun Janye Daga El-Fasher Saboda Kare Rayukan Fararen Hula

Babban hafsan hafsoshin Sojin Sudan kuma shugaban majalisar gudanar da mulkin kasar ya bayyana cewa; Rundunar sojin kasar ta bar birnin El Fasher ne domin

Babban hafsan hafsoshin Sojin Sudan kuma shugaban majalisar gudanar da mulkin kasar ya bayyana cewa; Rundunar sojin kasar ta bar birnin El Fasher ne domin gujewa “kisan fararen hula” da dakarun kai daukin gaggawa ke yi

Shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin Soja ta Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce: shugabannin sojoji sun yanke shawarar barin birnin El Fasher da ke Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan ne, domin kare birnin da ‘yan kasar daga afkawa cikin matsalar kisan kai a hannun Rundunar Rapid Support Forces ta dakarun Kai Daukin Gaggawa.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu, al-Burhan, wanda ke jagorantar rundunar sojin Sudan, ya ce a wani jawabi da aka watsa ta talabijin a gidan talabijin na gwamnati: “Kowa yana bin abin da ya faru a El Fasher, kuma shugabannin da ke can, ciki har da kwamitin tsaro, sun yanke shawarar cewa dole ne su bar birnin saboda halaka da kisan fararen hula.”

Ya bayyana cewa shugabannin sojoji a El Fasher “sun yanke shawarar barin birnin, kuma sun amince da fice daga cikinsa, bisa sharadin cewa za su bar birnin zuwa wuri mai aminci don ceton sauran ‘yan kasar da sauran birnin daga halaka.” Ya kara da cewa: “Wannan yana daya daga cikin matakan ayyukan soji da aka dora musu a matsayinsu na al’ummar Sudan, kuma koyaushe suna fadin hakan, kuma suna maimaitawa: al’ummar Sudan za su yi nasara, kuma Sojojin Sudan za su yi nasara.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments