Afrika ta Kudu Ta yi Gargadi Game Da Duk Wani Yunkuri Na Fitar Da Falasdinawa Daga Yankin Gaza

Ministan harkokin wajen kasar Afrika ta kudu Ronald lamola a jiya a joharnesbourg yayi gargadi game da kwaso falasdinawa da aka yi a baya bayan

Ministan harkokin wajen kasar Afrika ta kudu Ronald lamola a jiya a joharnesbourg yayi gargadi game da kwaso falasdinawa da aka yi a baya bayan nan yana nuna irin yunkurin da ake yi na tilasta musu barin yankin gaza, inda ya bayyan shirin a matsayin wani bangare na shirin korar falasdinawa daga gidajensu.

Pretoriya ta fitar da sanarwa na kokarin kwashe falasdinawa daga yankin Gaza zuwa kasar Afrika ta kudu, yayi gargadin cewa wannan matakin yana iya zama wani bangare ne na shirin iyakoki don tarwatsa falasdinawa da karyar canza musu wuri don basu taimakon Agaji

Minsitan harkokin wajen na afrika ta kudu ya bayyanawa manema labarai cewa batun shirin ajandar iyakoki na dauke falasdinawa daga gaza zuwa yankuna daban daban na duniya, yace Afrika ta kudu bata bukatar wani jirgi ya sake sauka a kasarta domin afili yake wani shiri ne na korar falasdinawa daga gaza da gabar yammacin kogin jodan

Yanzu haka dai jirage biyu ne suka sauka a afrika ta kudu dauke da daruruwan falasdinawa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments