Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida da kashi 30% na bangaren da harajin Amurka ya shafa a wannan makon, tare da kebe wasu ka’idojin samun wannan tallafin kudi.
Kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka ta kwashe watanni tana kokarin tattaunawa da Washington, inda ta yi tayin sayen iskar gas na Amurka da kuma zuba jarin dala biliyan 3.3 a masana’antun Amurka a wata yarjejeniya da tawagar shugaban Amurka Donald Trump ta gabatar. Wannan yunƙurin ya ci tura.
Jami’an Afirka ta Kudu sun ce, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters, harajin Amurka zai iya janyo asarar dubunnan ayyuka, musamman a fannin noma da kera motoci.
A wani taron manema labarai, ministocin ciniki da harkokin waje na Afirka ta Kudu sun ce ana samar da wasu hanyoyi wadanda za su taimaka matuka wajen rage radadin da harajin na Amurka kai iya haifarwa a bangarorin da abin ya shafa, kuma tuni an riga an fara gudanar da tsare-tsaren da suka dace kan hakan.
Ministocin biyu sun bayyana cewa Afirka ta Kudu ba ta haifar da wata barazanar kasuwanci ga tattalin arzikin Amurka ko tsaron kasarta, suna masu jaddada cewa “kayyakin da take fitarwa suna bisa tsarin cibiyar masana’antun Amurka kuma galibi ba sa gogayya da kayayyakin Amurka.”
Har ila yau, gwamnati na aiki kan shirin tallafi, wanda zai hada da manyan wuraren aiki, masana’antu da kuma hanyoyin da za a rage tasirin asarar ayyukan yi ta hanyar asusun inshorar tallafi ga ‘yan kasa.