Ministan ‘yan sandan kasar Afirka ta kudu, ya ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na cewa an yi wa fararen fatar kasar kisan kiyashi a yayin ziyarar da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya kai.
A yayin ganawar da ya yi da shugaban kasar Afirka ta kudu, shugaban kasar Amurka ya kunna wani faifen bidiyo da a ciki aka nuna gicciye a gefen hanya domin tunawa da fararen fata manoma da aka yi wa ksian gilla.
Ministan ‘yan sandan kasar ta Afirka ta kuku Senzo Mchunu ta cewa; Wadannan gicciyen ba su nuni da cewa suna akan kabarurruka ne, ko wani wuri na tunawa da matatu, an Sanya su ne a 2020 domin tunawa da dukkanin manoman da aka kashe a fadin kasar ta Afirka ta kudu.
Har ila yau, ministan ‘yan sandan na kasar Afirka ta kudun ya kuma kara da cewa; ‘yan fashi da makami sun kashe wasu ma’aurata manoma a cikin gonarsu, yana mai kara da cewa; Abinda Trump ya yi shi ne murguda wancan labarin da kirkirar abinda ya kira; “Kisan Kiyashi.”
Mchunu ya kara da cewa; kasar Afirka ta kudu tana girmama mutanen Amurka da shugaban kasarta, amma ko kadan ba ta girmama kirkirarren labarin; Kisan Kiyashi.”
Amurka ta dauki wannan matakin ne dai a kan Afirka Ta Kudu saboda ta kai karar HKI akan kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Falasdinu.