Afirka Ta Kudu Ta Bukaci A Tsagaita Wuta Cikin Gaggawa A Falasdinu da Lebanon

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bukaci da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Falasdinu da kuma Lebanon. A wani bangare na bayanin da ta

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bukaci da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Falasdinu da kuma Lebanon.

A wani bangare na bayanin da ta yi, Ma’aikatar hulda da kasashen duniya da hadin gwiwar kasa da kasa (DIRCO) ta Afirka ta Kudu ta fitar da wata sanarwa domin tunawa da ranar hadin kai da al’ummar Falasdinu karo na 47.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bi sahun kasashen duniya ne wajen bikin tunawa da ranar hadin kai da al’ummar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya, da kuma sabunta kudurin da Afirka ta Kudu ke da shi na ganin an warware matsalar Falastinu.

Kasar Afirka ta Kudu dai na ci gaba da jajircewa wajen ganin ta ci gaba da karfafa dankon zumunci da hadin gwiwa tsakaninta da Falasdinu tare da yin kira ga kasashen duniya da su yi aiki tukuru domin samar da zaman lafiya da kuma ba da goyon bayan jin kai, tattalin arziki da siyasa.

Dangane da yadda Isra’ila ke mamaye da Falasdinu ba bisa ka’ida ba, da kuma ta’asar da ake yi a kullum, kasar Afirka ta Kudu ta sake jaddada kiranta na tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Falasdinu da Lebanon, tare da kaddamar da tsarin siyasa don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Dole ne kasashen duniya su yi aiki tukuru don taimakawa al’ummar Palasdinu su cimma burinsu na samun ‘yanci, adalci da kuma ‘yantacciyar kasarsu Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments