Afirka ta Kudu na son yin hadin gwiwa da Najeriya a bangaren ayyukan ma’adanai

Shugaba Ramaphosa ya nuna sha’awar Afirka ta Kudu na yin hadin gwiwa da Najeriya don amfani da ma’adanai masu mahimmanci, musamman ma lithium, don ayyukan

Shugaba Ramaphosa ya nuna sha’awar Afirka ta Kudu na yin hadin gwiwa da Najeriya don amfani da ma’adanai masu mahimmanci, musamman ma lithium, don ayyukan samar da batura na motocin lantarki (EV).

Ya bayyana hakan ne a wannan Talata a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, a taron kasuwanci tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu.

Ya ba da shawarar yin amfani da dimbin lithium na Najeriya da ke kwance a karkashin kasa a matsayin ginshiki na kokarin habaka masana’antu a bangaren EV.

Ya bukaci kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyin hada-hadar kudi da su ci gaba da su hada kai wajen gina ababen more rayuwa da bunkasa karfin masana’antu a wannan fanni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments