Jam’iyyun siyasar kasar Afirka Ta Kudu sun nuna cikakken goyon bayansu ga Shirin shugaban kasar Cyril Ramaphosa na aikewa da sojoji zuwa yankunan da ake samun tashe-tashen hankula da kuma hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, domin su taimakawa ‘yan sanda.
A jawabin da ya gudanar ga al’ummar kasar daga birnin Cape Town a jiya Alhamis ya ce; Tsararrun Laifuka da ake yi a cikin kasar, suna daga cikin babban kalubale da ake fuskanta.
Bayanai suna nuni da cewa a kowace rana ta Allah ana kashe mutane 60 da su ka hada da fada a tsakanin kungiyoyin ‘yan daba a cikin garin Cape Town, haka nan kuma harbe-harben da ake yi masu alaka da wuraren hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Shugaba Ramaphosa ya kuma ce; Tsararrun laifuka da ake yi a cikin kasar su ne baranaza ta kusa da tsarin Demokradiyyarmu yake fuskanta, haka nan ci gabanmu na tattalin arziki.”
Ramaphosa y ace; Na bayar da umarni ga ministan ‘yan sanda da kuma rundunar tsaron kasa da su fito da tsarin aiki akan yadda za a kai jami’an tsaronmu zuwa yammacin Cape Town da kuma Gauteng a cikin kwanaki kadan masu zuwa.”
Mafi yawancin jam’iyyun siyasar kasar sun yi maraba da wannan matakin tare da yin jinjina ga shugaban kasar.
Jam’iyytar da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma yake jagroanta ce kadai ta nuna damuwa akan inda za a samo kudaden daukar nauyin wannan aikin.