Admiral Sayyari: Dole Ne Jami’an Tsaron Iran Su Kasance Cikin Shirin Ko-Ta  Kwana

Mataimakin kwamandan rundunar sojin kasar Iran mai kula da harkokin tsaro kasar ya bayyana cewa: Jami’an tsaron Iran suna cikin shirin ko ta kwana Mataimakin

Mataimakin kwamandan rundunar sojin kasar Iran mai kula da harkokin tsaro kasar ya bayyana cewa: Jami’an tsaron Iran suna cikin shirin ko ta kwana

Mataimakin kwamandan rundunar sojin kasar Iran mai kula da harkokin tsaron kasar Admiral Habibullah Sayyari ya jaddada cewa: Dakarun kasar da suka hada da sojoji da dakarun kare juyin juya halin Musulunci, da sauran rundunoni sun shirya tsaf domin tunkarar duk wata barazana ta ciki gida da waje da kuma tabbatar da ‘yancin kai da tsaron kasar.

Admiral Habibullah Sayyari wanda ya yi jawabi a ranar Asabar a birnin Rasht fadar mulkin lardin Gilan a wajen taro na biyu na tunawa da shahidai dubu 8 daga wannan lardin, ya yi ishara da yakin baya-bayan nan da gwamnatin Sahayoniyya ta kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai cewa: “Bai kamata a yi tunanin cewa, ana yaki ne da gwamnatin sahayoniyya ba kadai, a maimakon haka a bayanta akwai girman kan duniya, wanda yakar Saddam da Iran ta yi a zamanin yakin Iran da Iraki bayan samun nasarar juyin juya hali, a shekara ta 1980 zuwa 1988), yana da nufin an niyyar ruguza juyin juya halin Musulunci da kuma yankin Iran ne kawai.”

Admiral Sayyari ya ce makiya sun shiga fagen fama da dukkanin karfinsu da fasahar zamani a wannan yakin yana mai bayanin cewa: Tsawon kwanaki 12 na yakin, gwagwarmayar da mutane suka yi a fagen daga ya kawo cikas ga shirin makiya, a duk lokacin da al’ummar Iran suke fagen fama, makiya sun kasa cimma burinsu.

Hamas

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments