Adadin Wadanda Su ka Kwanta Dama A Gobarar Tashar Jirgin Ruwan Shahid Raja’i Sun Kai 21

Ministan harkokin cikin gidan Iran Askandar Mumini wanda ya kai Ziyara zuwa wurin da gobarar ta tashi ya sanar da cewa adadin wadanda su ka

Ministan harkokin cikin gidan Iran Askandar Mumini wanda ya kai Ziyara zuwa wurin da gobarar ta tashi ya sanar da cewa adadin wadanda su ka jikkata sun kai 750 da kuma wadanda su ka rasa rayukansu zuwa 14.

Sai dai kuma daga baya ma’aikatar shari’a ta kasar Iran din ta ta sanar da karuwar wadanda su ka kwanta dama zuwa 21

Mai shigar da kara na gundumar Hurzumgan, Mujtaba Kahraman ya sanar da cewa; Daya daga cikin aikin da suke yi shi ne tantance wadanda su ka su ka rasa rayukansu. Haka nan kuma ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu sun tabbatar da mutuwar mutane 21. Har ila yau ya bayyana cewa bayan tantance gawawwakin wadanda su ka rasa rayukansu za a mika su ga iyalansu domin yi musu jana”iza.

Biyu daga cikin wadanda aka tabbatar da mutuwarsu, mata ne sauran kuma maza ne.

A jiya Asabar ne dai aka sami fashewa mai karfi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’i da hakan ya yi sanadiyyar jikkata da kuma mutuwar mutane da dama.

Tuni aka bude bincike domin gano musabbabin abinda ya faru.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments