Adaidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 398 da adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sanadiyyar hare-haren sojojin mamaya sun haura 43,0000.
A jiya Alhamis ma dai Falasdinawa shaidai sun haura 30 a arewacin Gaza. Sojojin mamayar sun killace yankin Arewacin Gaza tare da kai hare-hare da manyan bindigogi a tsawon kwakani 34. Bugu da kari ‘yan mamayar sun hana masu ayyukan agaji dauko gawawwakin shahidai daga karkashin baraguzai.
A can yammacin kogon Jordan kuwa,kungiyar agaji ta “Red Crescent” ta sanar da cewa wani matashin Bafalasdine ya yi shahada, yayin da wasu 5 kuma su ka jikkata bayan da sojojin mamaya su ka kutsa cikin garin Tul-Karam.
A sansanin Jabaliya ma sojojin mamayar sun kai hare-hare da jiragen sama na yaki, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar adadi mai yawa na Falasdinawa da ba a tantance yawansu ba, saboda suna karkashin baraguzan gidajen da su ka fada a kansu.
Dama dai sojojin mamayar sun killace yankin na Arewacin na Gaza, tare da hana shigar da abinci ko magani a cikinsa, sannan kuma su na kai hare-hare akan mutanen da suke yankin. HKI tana son korar dubban mutanen da suke a yankin domin ta kafa wani yankin na tsaro.
Sai dai har yanzu mafi yawancin Falasdinawa sun ki ficewa daga gidajen nasu.