Sojojin HKI sun ci gaba da keta hurumin yarjeniyan tsagaita budewa juna wata tsakaninta da Gaza inda a jiya Lahadi kadai ta kashe Falasdinwa 14 a wurare daban-daban a yankin.
Tashar talabijin ta Almayadden ta kasar Lebanon ta bayyana cewa yawan shahidai a kan tafarkin Kudus a Gaza ya kai 48,872 da kuma wadanda suka ji rauni tun fara yakin ya karu zuwa 112,032.
Dan rahoton tashar al-mayadeen ya bayyana cewa a jiya Lahadi bafalasdiniya guda ta yi shahada a cikin gidanta a sansanin yan gudun hijira na Nusairat a lokacinda sojojin yahudawan suka bude wuta a kan gidanta.
Rahoton ya kara da cewa wani jirgin yakin da ake sarrafa shi daga nesa ya bude wuta kan wasu Falasdinawa a kauyen Hijru-ddik a tsakiyar zirin gaza na Gaza. Sannan rahoton ya kara da cewa wata tankar yakin HKI ta bude wuta kan wasu wurare a kauyen Al-qararah daga arewa masu gabacin garin Khan Yunus, inda nan ma da dama suka yi shahada.
Labarin ya kara da cewa an dauko shahidai 17, 8 daga cikinsu ba’a gano ko su waye ba, kuma suna daga cikin wadanda suka yi shahada tun lokacin yakin.