Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fitar da rahoton kididdiga na yau da kullun kan adadin Falasdinawa da suka yi shahada da wadanda suka jikkata sakamakon ci gaba da kai hare-haren wuce gona da irin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan yankin Zirin Gaza a rana ta 427 a jere, adadin wadanda suka yi shhada suka haura zuwa 44,612 yayin da wadanda suka jikkata suka kai 105,834, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 Miladiyya.
Har ila yau majiyar ma’aikatar lafiya ta sanar da cewa: Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun aiwatar da wani kisan kiyashi kan iyalai 3 a Zirin Gaza da suka kai ga shahadan Falasdinawa 32 tare da jikkatan wasu 95 na daban cikin sa’o’i 24 da suka gabata.