Firayim Ministan Habasha Abiy Ahmed ya yi kira da kasashen duniya su shiga Tsakani domin yin tsakanin kasarsa da Eritrea kan batun Tekun Ja, yana mai jaddada muhimmancin kawo karshen duk wata tashin tashina a yankin Kahon Afirka.
Abiy, yayin da yake jawabi ga majalisar dokoki a Addis Ababa, ya yi watsi da batun yin amfani da karfin soja amma ya jaddada cewa dole ne a saurari bukatar Habasha, kuma a warware batun ta hanyar diflomasiyya.
“Bukatar Habasha ita ce samun damar shiga teku, amma ba mu da niyyar shiga yaki da Eritrea. Akasin haka, mun gamsu cewa za a iya warware wannan batu ta hanyar lumana da fahimtar juna ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ba,” in ji Abiy.
Dangantaka tsakanin Habasha da Eritrea ta tabarbare a cikin ‘yan watannin nan, shekaru da dama bayan da Eritrea ta sami ‘yancin kai a shekarar 1993, inda ta balled aga Habasha bayan kai ruwa rana. Kasashen biyu sun yi yakin kan iyaka mai tsanani da aka zubar da jini daga 1998 zuwa 2000 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.
Duk da cewa Abiy ya sami kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2019 saboda daidaita dangantaka da shugaban Eritrea Isaias Afwerki, dangantaka ta kara yin tsami tun bayan kawo karshen yakin basasar Habasha na shekaru biyu a Tigray, inda sojojin Eritrea suka fafata tare da sojojin gwamnatin Habasha.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta kiyasta cewa rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 600,000.