Abdulmalik Husi: Wajibi Ne A Ladabtar Da Ashararai Uku Da Su Ne Amurka, Birtaniya Da HKI

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi wanda ya gabatar da jawabi a ranar kasar Yemen ta gwgawarmaya, ya yi suka akan yadda

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi wanda ya gabatar da jawabi a ranar kasar Yemen ta gwgawarmaya, ya yi suka akan yadda shugabannin kasashen larabawa su ke yi wa siyasar Amurka makauniyar biyayya, tare da cewa hakan yana cutar da kasashensu ne.

Bugu da kari Sayyid Abdulmalik al-Husi ya jinjinawa masu kare Falasdinawa, da su ka hada kasar Iran, kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, da kuma ‘yan gwgawarmayar Iraki.

Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya kuma yi ishara da yadda Amurka, Birtaniya da HKI suke kai wa Yemen hari saboda kariyar da take bai wa al’ummar Falasdinu, tare da bayyana cewa, da akwai abubuwa mamaki da za su faru a nan gaba.

Har ila yau Sayyid Abdulmalik al-Husi ya gargadi masu kai wa Yemen din hari, da cewa sojojin Yemen za su yi amfani da makamai na karshe na zamani da suke da su akansu.

Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya kuma bayyana dalilin kai wa Yemen hari da cewa, shi ne kunna wutar yaki a cikin wannan yankin baki daya.

Sayyid Abdulmalik Husi ya kuma ce; Kasarsa ba tad a rikici da wata daga cikin kasashen larbawa ko na musulmi, illa iyaka suna fada ne da Amurka, Birtaniya da HKI saboda wuce gona da irinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments