A yau Take Ranar Arafa A Kasar Saudiya, Inda Mahajjata Kimani Miliyon 2 Suka Yi Tsayuwar Arafa

A yau Asabar ce musulmi mahajjata suka kammala tsayuwar a Arafa, wanda ya kasance rukuni daga cikin rukunan ayyukan Hajji. Kamfanin dillancin labaran Iran Press

A yau Asabar ce musulmi mahajjata suka kammala tsayuwar a Arafa, wanda ya kasance rukuni daga cikin rukunan ayyukan Hajji.

Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP ya bayyana cewa mahajjata daga ciki da kuma wajen kasar saudiya, mahajjata kimani miliyon 2 ne suka sami damar yin aikin hajja a wannan shekarar.

A jiya Jumma’a ce dai mahajjatan suka fara ayyukan Ibadan Hajji in da suka kwararo daga Makka zuwa Minna, sannan daga Minna suka wuce zuwa Arafa a safiyar yau Asabar, inda suka yi yina suna addu’o’i da ambaton All..T,  a kusa da duten ‘Rahama da ke filin Arafa a wajen birnin Makka.

A nan arafa ne manzon All..(s) ya yi daya daga cikin khudubobinsa na karshe, a rayuwarsa, inda kuma yayi bankwana da musulmi. A cikin khudubarsa ya kodaitar da musulmi kan hadin kai da kuma rashin rarraba a bayansa. Sannan ya kodaitar kan adalci da kuma tausayawa juna shekaru 1,435 da suka gabata.

Banda tsayuwar Arafa dai ayyukan da suke gaban mahajjan sun hada da kwana a musdalifa, da jifan shaitan a gobe Lahadi da yanka da iski ko rage gashi, da dawafi, da kuma sauran ayyukan hajji a Mina na kwanki biyu zuwa 3 masu zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments