Daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akwai wani kwamanda na dakarun kare juyin musulunci na Iran Birgediya Janar Muhammad Riza Zahedi, da mataimakinsa Mhammad Haji Rihimi, sai kuma wasu mutane biyar da suke a tare da su.
Daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akwai jami’an ‘yan sandan kasar Syria biyu kamar yadda majiyar tsaro ta ambata.
Jakadan Iran a Syria ya ce; Iran Za Ta mayar da martani akan harin, domin HKI ba ta aiki da dokokin kasa da kasa.