A Jiya Laraba Ce Iran Take Bukukuwan Cika Shekaru 78 Da Kwatar Kamfanin Man Fetur Na Kasar Daga Hannun Turawan Burtaniya

A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da

A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da taimakon gwamnatin lokacin suka sami nasarar kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar, daga hannun wani kamfanin mai na kasar Burtaniya suka maida shin a kasa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce , wannan rana abin alfakhari ne ga mutanen kasar, don bayan haka ne kasar ta sami ikon kawo ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma shimfida harsashen samun yencin kasar daga hannun kasashen yamma wadanda suka mamaye bangarori da dama a cikin al-amuran kasar.

A ranar 19 ga watan Maris na shekara ta 1951 ne, wato shekaru 78 da suka gabata,  firai ministan kasar Iran na lokacin Dr Muhammad Musaddiq tare da taimakon malaman addini ya sami nasarar kwace kamfanin man fetur na kasar daga hannun turawan ingila ya maida shi na kasa.

Majalisar dokokin kasar Iran ta amince da dokar maida kamfanin ya zama ta kasa a ranar 17 ga watan Maris na shekara ta 1951, sannan majalisar dattawan kasar ta amince da Ita a ranar 19 ga watan Maris na shekarar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments