A Gobe Litinin Za A Yi Atisayen Sojan Ruwa Na Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashen Iran, Rasha Da China

Kamfanin dillancin labarun “ Irna” ya nakalto cewa; Jiragen ruwa na soja da kuma dakarun kare juyin musuluni na Iran za su shiga cikin atisayen

Kamfanin dillancin labarun “ Irna” ya nakalto cewa; Jiragen ruwa na soja da kuma dakarun kare juyin musuluni na Iran za su shiga cikin atisayen na hadin gwiwa da kasashen Rasha da kuma China.

Bugu da kari da akwai wasu kasashen da za su turo sojojin masu sa ido, da su ne; jamhuriyar Azerbaijan, Afirka Ta Kudu, Oman, Khazakistan da Pakistan. Sai kuma kasashen Katar, Iraki, HDL da kuma Srilanka.

Wannan atisayen dai za a yi ne a sansani na uku na sojan ruwan Iran wanda yake a arewacin tekun Indiya.

Manufar wannan atisayen dai shi ne  bunkasa yadda kasashen za su rika aiki tare a tsakanin kasashen sojojin ruwan Iran, Rasha da kuma China.

Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin ruwan kasashen Iran Rasha da kuma China su ka yi atisayen soja na hadin gwiwa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments