Akalla falasdinawa 6 ne suka yi shahada a wani harin da sojojin HKI suka kai kan gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye.
Daga cikin wadanda suka kashe har da wata mata diyar shekara 80 a duniya.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yahudawan sun cilla albarusai a kan kirjin matar wadanda suka yi sanadiyyar shahadarta.
Yawan falasdinawa wadanda suka yi shahada a Gaza kadai a cikin watanni 14 da suka gabata ya wuce dubu 45, banda haka akwai dururuwan Falasdinawa da suka kashe a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye.
Labarin ya kara da cewa duk kokarin da aka yi don dakatar da kasashen duniya suka yi na kawo karshen tsagaita wuta a Gaza, gwamnatin Amurka ta hana hakan faruwa a kwamitin tsaro na MDD.