Mutane miliyan 21.48 ne suka halarci tarukan Arba’in a Karbala a wannan shekara

Miliyoyin Masu ziyara ne daga sassa daban-daban na duniya suka birnin Karbala na kasar Iraki a yayin gudanar da tarukan ziyarar Arba’in na wannan shekara,

Miliyoyin Masu ziyara ne daga sassa daban-daban na duniya suka birnin Karbala na kasar Iraki a yayin gudanar da tarukan ziyarar Arba’in na wannan shekara, kamar yadda hukumomi a karbala suka sanar.

Wani babban jigo daga cikin masu kula da Hubbaren Sayyiduna Abbas a Karbala ya tabbatarwa gidan talabijin na Press TV cewa, akalla mutane miliyan 21.48 daga kasashe da dama ne suka hallara a Karbala domin tunawa da ranar Arba’in, wato cikar kwanaki 40 bayan shahadar Imam Husaini (AS) jikan Annabi Muhammad (SAW) A ranar Ashura.

“Jimillar adadin masu ziyara ya kai 21,480,525”, in ji cibiyar da ke kula da hubbaren Abbasi da ke da alhakin tattara alkalumma na adadin halartar wadannan taruka.

Daga cikinsu akwai kimanin maziyarta Iraniyawa miliyan 3.5, kamar yadda alkalumman da aka bayar a Tehran suka nuna.

Taron Arba’in na daya daga cikin manya-manyan tarukan addini a duniya, kuma babban taron musulmi da yafi hada mutane masu yawa a wuri guda a duniya.

Masu ziiyara a wannan shekara sun fito ne daga kasashen Iran, Afganistan, Azarbaijan, Bahrain, Kuwait, Pakistan, Saudiyya, Syria, India da sauran kasashe daga nahiyar Asia, Turai, Afirka, Amurka da Australia.

Mahajjata sun yi tattaki ne zuwa birnin mai alfarma domin samun damar ziyartar hubbaren Imam Husaini (AS) da ke Karbala a kudancin Iraki.

An binne Imam Husaini da dan uwansa Abbas bn Ali a wannan wuri tare da sauran sahabban Imam hussaini da iyalansa da suka yi shahada tare da shi a Karbala a ranar Ashura.

A bana, abubuwan da suka faru wadanda suka fi daukar hankula sun hada da daga tutocin Falasdinawa da masu ziyara suka rika yi, domin nuna goyon baya ga al’ummar Gaza, da kuma yin tir da Allah wadai da kisan kiyashin Isra’ila a kan al’ummar Gaza marasa kariya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments