Arba’in Na Imam Hussain (a) Abin Alfakhari Ne Ga Duniyar Musulmi Kuma Sakon Hadin Kai Ne Garesu

Shugaban jami’ar Loristan a nan tsakiyar kasar Iran ya bayyana cewa taron 40 na Imam Hussain (a) a karbala, wani abun alfkhari ne ga musulmi

Shugaban jami’ar Loristan a nan tsakiyar kasar Iran ya bayyana cewa taron 40 na Imam Hussain (a) a karbala, wani abun alfkhari ne ga musulmi a duniya kuma taron yana iya zama sanadiyyar hadin kan al-ummar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya nakalto Dr Ali Nazari shugaban Jami’ar Loristan yana fadar haka a wata hira da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran IRNA, ya kuma kara da cewa, taron 40 na Imam Hussain (a) daya ne daga cikin ibadu mafi girma da musulmi suke da shi, ya kuma kara da cewa tattakin 40, wani al-amari ne wanda yake nuna karfin musulmi da musulmi, sannan kuma hadin kansu a duniya ne. Ya ce, musulmi suna amfani da damar da suka samu ta 40 na Imam Hussain (a) don nuna goyon bayansu ga mutanen Gaza wadanda ake zalunta.

Sannan Nazari ya kammala da cewa, musulmi da dama yau suna dauke da hotunan shahidan Gaza da sauran shahidan ‘kawancen masu gwagwarmaya’ a yankin don bayyana wannan goyon bayan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments