A dai dai lokacinda ake gudanar da taron majalisar tsaron kasa ta Amurka, makaman roka sun fada kan sansanin sojojin kasar da ke Ainul Asad a kasar Iraki, kuma rahotanni sun bada sanarwan halakar sojojin Amurka da dama wasu kuma sukam ji rauni
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto “dakarun Alwa’adul-Haaq’ daya daga cikin kungiyoyi wadanda suke gwagwarmaya da mamayar da Amurka takewa kasar Iraki, suna cewa sojojin Amurka 6 ne suka halaka, a yayinda wasu 9 suka je rauni.
Amma wata majiyar labarai ta HKI ta bayyana cewa sojojin Amurka biyu ne suka halaka a farmakin. Kungiyoyi masu gwagwarmaya da ayyukan ta’addanci a kasar Iraki wadanda ake kira Hasdushaabi, su kan kaiwa sojoji Amurka a kasar Iraki da nufin korarsu daga kasar.
Har’ila yau dakarun na kasar Iraki suna kaiwa sojojin Amurkan hare hare don tallafawa mutanen Gaza wadanda sojojin yahudawan Sahyoniyya suke kashe wa a kasar Falasdinu da suka mamaye.
Ma’aikatar yaki a Amurka ‘Pentagon’ ta tabbatar da wannan labarin ta kumam kara da cewa tana gudanar da bincike don gano irin asarorin da aka yi sanadiyyar faduwar rokoki a kan sansanin sojojinta a Ainul Asad.