Gwamnatin Amurka ta kara tura wasu Karin makamai zuwa HKI don kareta daga daga duk wata barazana bayan kisan da ta yiwa shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban Biden yana cewa kissan Haniyya ba zai taimaka wa kokarin tsagaita wuta a Gaza ba. Amma kuma a lokaci guda ya bada umurnin a tura Karin makamai zuwa HKI don kareta daga duk wata barazana gareta kan abinda ta aikata.
Labarin ya kara da cewa bayan kissan Haniya shugaba Biden ya zanta ta wayar tarho da Benyamin Natanyahu Firaiministan HKI kan wannan batun.
Sun kuma kara da cewa yahudawan na shirin, don fuskantar duk wani maida martanin daga JMI dangane da kissan Haniyya da kuma, Hizbullah dangane da kissan wani babban kwamandan sojojinta a birnin Beirut.
A ranar laraban da ta gabata ce HKI ta kashe shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a dai dai lokacinda yake halattar bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan a birnin Tehran.
Banda haka HKI ta kashe wani babban kwamandan sojojin Hizbullah Sayyid Fu’ad Ali Shukr a ranar Talatan da ta gabata a birnin Beirut babban birnin kasar ta Lebanon. Dukkan kasashen kawancen gwagwarmaya dai, sun sha alwashin daukar fansar kashe kashen na wadannan manya manyan jagogorin su.