Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jagoranci Sallar Jana’izar Isma’il Haniyah A Tehran

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jagoranci sallar jana’izar shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas shahidi Isra’il Haniyeha a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Rahotonni

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jagoranci sallar jana’izar shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas shahidi Isra’il Haniyeha a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran

Rahotonni sun bayyana cewa:  Sakamakon cincirondon dubban daruruwan jama’a, an kai gawar Isma’il Haniyeh zuwa babban dandalin ‘yanci na Azadi da ke birnin Tehran, inda bayan sallar gawan za a tafi da ita zuwa kasar Qatar don binne shi a can.

Dubban daruruwan masu makoki ne suka taru a tsakiyar babban birnin kasar Tehran, dauke da hotunan Haniyeh da tutocin Falasdinu domin gudanar da sallar jana’izar shahidi Isma’il Haniyah a yau Alhamis.

Bayan kammala sallar, dimbin jama’a ne suka raka gawar Haniyeh da mai tsaron lafiyarsa cikin gangami zuwa wajen taron makokinsa mai nisan kilomita 5 kafin gudanar da shirye-shiryen daukar gawar zuwa kasar Qatar, inda za binne shi a can.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments