Isra’ila Ta Sake Kashe Wani Adadi Mai Yawa Na Mata Da Kananan Yara  A Gaza

Sojojin Isra’ila sun kashe ƙarin Falasɗinawa 41 a hare-hare da suka kai a Gaza, abin da ya sa adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a

Sojojin Isra’ila sun kashe ƙarin Falasɗinawa 41 a hare-hare da suka kai a Gaza, abin da ya sa adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a yankin ya kai 39,258 tun daga 7 ga watan Oktoba, a cewar Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta yankin.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ƙara da cewa mutum aƙalla 90,589 ne suka jikkata sakamakon hare-haren.

“Dakarun Isra’ila sun kashe mutane 41 tare da jikkata 103 a hare-haren ƙare-dangi da suka kai wa wasu iyalai a awanni 24 da suka wuce,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa, “Har yanzu akwai mutane da dama a ƙarkashin ɓaraguzan gine-gine da kuma kan hanyoyi domin kuwa masu aikin ceto sun kasa isa gare su.”

Akalla yara 15 da mata 8 na daga cikin Falasdinawa 31 da aka kashe a wani harin da Isra’ila ta kai a makarantar Khadija da ke Deir al-Balah da ke tsakiyar zirin Gaza, kamar yadda ofishin yada labaran gwamnatin Falasɗinawa ya sanar a ranar Asabar.

Tun da farko, ofishin yada labaran gwamnatin Gaza ya ce Falasdinawa 31 da suka hada da yara kanana ne suka mutu yayin da wasu 100 suka jikkata a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari a makarantar, wadda kuma ta kasance asibitin filin.

A cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran ya fitar ya bayyana cewa, makamai masu linzami guda uku sun afka wa wani wurin da ya kasance mafakar dubban mutanen da suka rasa matsugunansu.

Sojojin Isra’ila sun amince da kai harin a safiyar ranar Asabar, suna masu ikirarin cewa tana dauke da cibiyar kwamandojin kungiyar Hamas, a cewar wata sanarwa daga kakakin rundunar Avichay Adraee.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments