Amurka: Sanata Bernie Sanders Ya Shelanta Natanyahu A Matsayin Mai Laifukan Yaki Kuma Makaryaci

A dai dai lokacinda firai ministan HKI Benyamin Natanyahu yake jawabi a gaban majalisar dokokin kasar Amurka a jiya Laraba, sanata Bernie Sanders ya kira

A dai dai lokacinda firai ministan HKI Benyamin Natanyahu yake jawabi a gaban majalisar dokokin kasar Amurka a jiya Laraba, sanata Bernie Sanders ya kira shi da sunan ‘Mai laifuffukan Yaki’ kuma makaryaci.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sanders yana fadar haka a shafinsa na X a yau Alhamis ya kuma kara da cewa, a karon farko a majalisar dokokin kasar Amurka an kawo wani  mai laifuffukan yaki yana jawabi a cikinta, kuma wasu suna sauraronsa.

Sanatan Sanders ya kara da cewa, Natamyahu ya zo majalisar dokokin Amurka ko Congress ne saboda ya gyara wa kansa siyasarsa ta cikin gida a HKI, don da dama daga cikin yahudawan HKI suna bukatar ya sauka. Ya ce Natanyaho mai aikata laifukan yaki ne, saboda ya bada umurnin a toshi dukkan hanyoyin shigar da abinci da magunguna zuwa yankin zirin Gaza, sannan yana kashe dubban yara da mata a yakin da sojojinsa suke fafatawa a Gaza.

Sanders ya shahara da aibata Natanyahu tun da dadewa, da kuma siyasar kasar Amurka danganne da HKI, ya ce dole ne gwamnatin kasar Amurka ta sauya siyasarta dangane da HKI, musamman kuma a bangaren take hakkin bil’adama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments