Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu sun rufe hanyoyin isa ofishin ma’aikatar harkokin waje a London

Wakilin tashar Al Mayadeen a birnin Landan ya bayar da rahoton cewa, masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu sun toshe hanyoyin shiga ma’aikatar harkokin wajen birnin

Wakilin tashar Al Mayadeen a birnin Landan ya bayar da rahoton cewa, masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu sun toshe hanyoyin shiga ma’aikatar harkokin wajen birnin London domin nuna adawa da matakin da sabuwar gwamnatin jam’iyyar Labour ta dauka na sauya manufofin Birtaniya kan harin da Isra’ila ke kai wa Gaza, da nuna adawa da yadda Birtaniya ke ci gaba da baiwa Isra’ila makamai , bayan watanni tara na yakin kisan kare dangi da aka yi wa yankin.

Ya ce, masu zanga-zangar sun haifar da wani sabon mataki na matsin lamba ga gwamnati. An bayyana muhimmancin zanga-zangar ta wurin da yake a hedkwatar hukuma da ke da alhakin tsara manufofin ketare na Burtaniya.

Rahoton  ya bayyana cewa, ‘yan sandan kasar Birtaniya sun sanya wa masu zanga-zangar shingaye  domin hana su ci gaba da zanga-zangar, inda suka yi yunkurin tarwatsa su da karfin tuwo, tare da kame da dama daga cikinsu.

Zanga-zangar ta zo ne kwana guda bayan da Declassified UK ta bayyana cewa ma’aikatar tsaron Burtaniya ta mallaki faifan bidiyo na sa ido kan Gaza daga ranar da “Isra’ila” ta kashe ma’aikatan agaji na kasa da kasa bakwai a wani kisan gilla amma ta ki sakinta, saboda tsoron za a yi amfani da shi a matsayin shaida a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

Hotunan, wanda jirgin saman sa ido na Royal Air Force (RAF) ya dauka, ya tattara kusan sa’o’i biyar a kan Gaza a ranar 1 ga Afrilu, lokacin da “Isra’ila” ta kashe mutane bakwai da ke aiki da ayarin abinci na duniya , ciki har da wasu tsoffin sojojin Burtaniya uku: John Chapman , James Kirby, da James ‘Jim’ Henderson.

Da alama dai jirgin na sa ido na RAF ya koma sansaninsa da ke Cyprus ‘yan mintuna kadan kafin kaddamar da harin.

Sakamakon haka, RAF na iya yin rikodin faifan abubuwan da suka faru da suka kai ga kisan kiyashin, wanda zai iya ba da haske kan ikirarin Isra’ila ta hanyar tabbatar ko akasin hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments